Home Blood Donation Matasa Musulmi yan Ahmadiyya za su tattauna akan zaman lafiyar kasa a...

Matasa Musulmi yan Ahmadiyya za su tattauna akan zaman lafiyar kasa a taronta na shekara-shekara na 45

3254
47
SHARE

Matasan Jama’ar Musulmi Ahmadiyya ta Nijeriya za su hadu a Zariya ta jihar Kaduna domin tattaunawa akan muhimman abubuwa wadanda musamman suka shafi matsalar kasa. Taron shekara-shekara wanda aka saba gudanarwa tun 1972 zai gudana a wannan shekarar daga ranar Alhamis 29 ga watan Maris zuwa ranar Lahadi 1 ga watan Afrilu na 2018, a makarantar Al-huda-huda ta Zariya a Jihar Kaduna. Taron yana da taken: Zaman lafiya a kasa: Abu ne da ake tsananin bukata a wannan zamani.

Za a tattauna matsayin matasa, musamman gagarumar gudummuwar da suke bayarwa wajen gina kasa da cigabanta. Babban mai jawabi a wajen taron shi ne, Shahararren malamin nan kuma malamin Jami’a da ke Jami’ar Bayero ta Kano, wato Barista Badr Muhammad Basheer. Zai gabatar da makalarsa mai taken: Zaman Lafiya a kasa: Abu ne da ake tsananin bukata a wannan Zamani.

Wasu abubuwan da za a gudanar a wajen wannan taron sun hada da gwaje-gwajen lafiyar jama’a da ba da magunguna kyauta, a fadar Sarkin Zazzau. Sai Muhazara mai taken: Annabi Muhammadu (saw): Tauraron haskaka zaman lafiya ga al’ummah, wadda Malam Is’haq Habeebullah zai gabatar.

Sa’ar nan kuma matasa Musulmi Ahmadiyya za su gudanar da aikace-aikace na kawo cigaban gari, a Zariya tare da zagaya gari cikin lumana.

Daga cikin manufofin Majlis Khuddamul Ahmadiyya da aka kaddamar a Nijeriya a 1972 akwai tarbiyyantar da matasa kan tafarkin addini da ilimin zamani. Tana kuma kokarin ganin cewa matasan kungiyar sun ginu kan tsoron Allah, da gaskiya da adalci, domin su iya ba da gagarumar gudummuwa ga cigaban kasa. Kirarin Majlis Khuddamul Ahmadiyya shi ne: Kasa ba za ta gyaru ba, sai da gyaruwar matasa

Domin cikar wannan kirari nata, Majlis Khuddamul Ahmadiyya ba ta takaita ayyukanta ga Musulmi kadai ba, tana kai gudummuwarta ga kowa ba tare da nuna bambancin addini, ko launin fata, ko harshe ko akida ba. Kuma tana hada kawunan mabiya addinai daban-daban domin habaka zaman lafiya. A wajen taron na wannan shekarar, Matasan Ahmadiyya za su yi musabakar karatun Kur’ani, da tafka muhawara da wasanni da ka-ci-ci-ka-ci-ci  da sauransu.

Manyan baki da za su halarci taron sun hada da, gwamnan Jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-rufai, da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, da Amir na Jama’ar Musulmi Ahmadiyya ta Nijeriya, Dr. Mashood Aderele Fashola, shugaban Malaman Jama’ar Musulmi Ahmadiyya na Nijeriya, Maulana Afzal Rauf Ahmad. Sa’anan akwai su Prof. AbdulRahim Giwa daga Jami’ar Ahmadu Bello dake  Zariya, da Dr. Saheed Timehin daga Jami’ar Lagos, Sai Malam Nurudeen Okubena da shugaban kungiyar matasan kasar Nijeriya, da komishinan matasa da wasanni na Jahar Kaduna, da wakilai daga hukumar ‘yan sanda ta Kaduna, da wakilai daga ma’aikatar matasa da wasanni, da kuma shugabanin kungiyoyin addinai daban-daban.

Sa’ar nan kuma akwai kyaututtuka na musamman ga jihohi da bangarorin da suka taka rawar gani a wajen tafiyar da aikace-aikacen kungiyar, a matakai daban daban. Wadannan kyaututtuka sun kunshi sakamakon hidimomin da aka gudanar ne a shekarar da ta gabata kadai.


SIGNED

Saheed Kunleola Aina
SADR (National President)  

###
Contact for more information:

AbdulGaniyy Adiamoh
Phone Number: (+234) 7056547478,
Email Address: info@khuddam.ng
Website: www.khuddam.ng/ijtema
Twitter: www.twitter.com/muslimyouthnga
Facebook: www.facebook.com/khuddamnigeria
Instagram:  www.nstagram.com/khuddamnigeria

 

 

47 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here